Game da labarin cewa Sinawa fiye da 300 sun ratsa kan iyakar kasar kuma sun bi ta kasar Malaysiya da nufin shiga ayyukan ta'addanci da kungiyar IS ke gudanar, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying ta jaddada matsayin da kasar ke dauka, a ganawarta da manema labarai a ranar jumma'ar nan 23 ga wata a nan birnin Beijing.
Madam Hua ta ce Sin na nacewa ga yaki da ta'addanci, kuma kasar tana fatan kara hadin gwiwa da kasa da kasa ta fuskokin yaki da ta'addanci da tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro a duniya baki daya.
An ba da labari cewa, cikin 'yan shekarun baya, dimbin 'yan ta'addan ciki hadda Sinawa sun bi ta kasashen Malaysia da Indonesiya, domin zuwa kasar Turkiya inda kuma suka ratsa iyakokin Turkiya da Sham don shiga yankin dake karkashin kungiyar IS. Ministan harkokin cikin gida na kasar Malaysia Ahmed Zahid Hamidi ya bayyana cewa, Sin da Malaysia na mai da muhimmanci sosai kan batun da ke shafar tsaron kasa tare da yin alkawarin daukar matakai da za su wajaba don warware wannan matsala. (Amina)