Dangane da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya ce, a halin yanzu, 'yan ta'addan gabashin Turkistan na haifar da kalubalen tsaro a jihar Xinjiang, kuma haka ba kawai babban kalubale ne na tsaro da zaman karko ga kasar Sin ba, kalubalen tsaro ne ga gamayyar kasa da kasa. Aikin yaki da ta'addanci alhaki ne da ya rataya a wuyan gamayyar kasa da kasa, kasar Sin na son yin hadin gwiwa da kasashen da abin ya shafa kan wannan aiki da kuma yaki da 'yan ta'addan gabashin Turkistan. (Maryam)