Bisa gayyatar da shugaban taron dandalin tattaunawar tattalin arziki na kasa da kasa mista Klaus Schwab da kuma gwamnatin kasar Switzerland suka yi masa, firaministan kasar Sin mista Li Keqiang zai halarci taron shekara-shekara na taron dandalin na shekarar 2015 a birnin Davos na Switzerland wanda za a yi daga ranar 20 zuwa 22 ga wata, tare da yin ziyarar aiki a kasar.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei shi ne ya fadi haka a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing. Ya kara da cewa, firaministan kasar Sin zai halarci cikakken zama na taron dandalin tare da yin jawabi na musamman, inda kuma zai yi mu'amala da tattaunawa da wakilan hukumomin masana'antu da kasuwanci na kasa da kasa, tare da ganawa da mista Schwab.
Har wa yau firaministan na kasar Sin zai bayyana ra'ayinsa kan halin da kasashen duniya suke ciki, tare da yin karin bayani kan halin da kasar Sin ke ciki ta fuskar tattalin arziki da matakan da kasar ke aiwatarwa game da zurfafa yin gyare-gyare a gida. (Tasallah)