A yayin ziyarar aikin, firaminista Li ya ce ana kokarin neman bunkasuwa ba tare da la'akari da bambance-bambance ba, bisa wannan buri ya zama dole a kyautata yanayin rayuwar ma'aikata 'yan cin rani, da na masu fama da talauci a birane. Kana a samar da wani muhallin kasuwanci, da zai bude kofar takara cikin daidaito, da kwazo na samar da hidima ta zaman daidai wa daida ga jama'a, ta yadda za su iya karfafa fatansu game da rayuwarsu a nan gaba.
Firaminista Li ya nanata tambaya ga mazauna yankin game da ra'ayinsu kan gyare-gyaren tsoffin gidaje masu hadari. Bayan kuma samun amincewarsu, Mr. Li ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnatin yankin ta gaggauta gudanar da wannan aiki domin biyan bukatun jama'a, yana mai fatan cewa, mazauna wurin za su kasance cikin sabbin gidajensu, a yayin ziyararsa ta nan gaba. (Bilkisu)