in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hamas da Fatah sun amince da komawa teburin shawarwarin neman sulhu
2014-02-10 10:52:58 cri

Kungiyar Hamas dake ikon zirin Gaza, ta bayyana amincewarta a ranar Lahadi domin fadada shawarwari tare da kungiyar Fatah a cikin tsarin ingiza ayyukan sasanta bangarorin na Palesdinu dake gaba da juna.

Bayan ganawa tare da wata tawagar manyan jami'an kungiyar Fatah dake ziyarar aiki a birnin Gaza, shugabannin Hamas da na Fatah sun amince da yin kokari tare domin shirya yarjejeniyar sasantawa ta dindindin domin kawo karshen rashin jituwar siyasa ta tsawon shekaru bakwai.

Da yake magana gaban manema labarai bayan ganawar, mista Nabil Shaath, mamban babban kwamitin Fatah ya nuna cewa, kawo karshen rashin jituwa ta hanyar kafa wata sabuwar gwamnatin hadin kai da kuma shirya zabubuka cikin adalci sun kasance wajibi ga yawancin Palesdinawa. Haka kuma ya yi amfani da wannan dama domin yin kira ga Palesdinawa da su ba da azama domin tabbatar da hadin kai da zaman jituwa cikin kasa.

Fatah da Hamas sun kai ga cimma yarjejeniyoyi sasantawa guda biyu a karkashin jagorancin kasar Masar da Qatar a shekarar 2011 da shekarar 2012. Amma kuma har yanzu, wadannan yarjejeniyoyi biyu, ba'a aiwatar da su ba dalilin sabani kan batun tsaro da batun kawo gyaran fuska kan kungiyar neman 'yancin palesdinawa da Fatah ke da rinjaye.

A nasa bangare, Khalil al-Hayya, jami'in Hamas ya sheda wa manema labarai cewa, jam'iyyarsa na fatan cimma hadin kan 'yan kasa da daukar muhimman matakai domin rage gibin dake tsakanin bangarorin biyu. Haka kuma ya bayyana goyon bayansa ga shugaban Palesdinu Mahmoud Abbas, da ya yi watsi da bukatun Isra'ila da Amurka game da shawarwarin zaman lafiya na yanzu.

Kungiyar Hamas ta karbe ikon zirin Gaza ta hanyar zabubuka bayan yakin basasa a shekarar 2007 tare da kungiyar Fatah, dake ikon Cisjordanie a halin yanzu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China