Kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta yi watsi da haramcin wata kotun Masar wacce ta yanke hukuncin haramcin dukkanin harkokin kungiyar a yankin kasar Masar.
Kungiyar gwagwarmayar Palasdinawan wacce ta kasance tana mulkin zirin Gaza tun shekara ta 2007, ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, yanke hukuncin kotun wani abu ne dake da nasaba da siyasa, wanda aka yi domin a muzgunawa jama'ar Palasdinu a sakamakon fafutukar da Palasdinawan ke yi saboda mamayewar Isra'ila.
Kakakin kungiyar Hamas dake Gaza, Sami Abu Zuhri, ya yi Allah wadai da hukuncin kotun, yana mai cewar, zai yi illa ga fafutikar Palasdinawa kuma hakan zai kawo illa ga kasar Masar da kuma rawar da take takawa.
Kakakin kungiyar ta Hamas ya kara da cewa, yanke hukuncin baya da wani amfani, musamman da yake kungiyar ta Hamas ba ta da cibiyoyi da ofisoshi a birnin na Alkhahira, kuma harkokin kungiyar ta Hamas sun kasance kawai a yankunan Palasdinawa.
Kakakin kungiyar ta Hamas Sami Abu Zuhri, ya kaucewa yin sharhi akan yadda alakar za ta kasance tsakanin Hamas da kuma sabuwar gwamnatin Masar, to amma ya ce, kungiyar Hamas na sa ran fuskantar kalubale rashin adalci, a yayin da ake kara tsaurara matakan tsaro a zirin na Gaza.
Kamfanin dillancin labarai na Masar, Al-Sharq el-Awsat, tun farko ya ce, kotun dake Masar ta ba da umurnin haramta dukkanin harkokin kungiyar gwagwarmayar Hamas, tare da rufe daukacin ofisoshinta a kasar ta Masar. (Suwaiba)