Wani mamban kungiyar Hamas ta Palesdinu da ke sarrafa zirin Gaza ya bayyana a ran 3 ga wata cewa, 'yan rukunin 'Ezz el-Deen al-Qassam Brigades' da ke karkashin shugabancin kungiyar Hamas sun yi ganimar wani jirgin sama maras matuki a ciki na kasar Isra'ila wanda ya fadi a yankin da ke arewacin zirin Gaza, amma bai fayyace dalilin faduwar sa ba.
Bangaren soja na Isra'ila ya amince da wannan labari, inda suka bayyana cewa, jirgin ya fadi ne sakamakon matsalar sashen jikinsa.
A 'yan kwanakin baya, an kara samun tashin hankali a gabar zirin Gaza, dakarun Hamas da sojojin Isra'ila sun yi musanyar wuta, dakaru 4 na Palesdinu sun mutu sakamakon luguden igwoyi da farmakin jirgin sama da Isra'ila ta kai musu.(Danladi)