Kungiyar Hamas da wasu gungun mayakan Falasdinawa sun amince cikin daren Laraba da wata bukatar tsagaita bude wuta domin aikin jin kai ta sa'o'i biyar tare da Isra'ila da MDD ta gabatar. Hamas da wasu gungun mayakan Falasdinu sun amince da dakatar da harba rokoki zuwa Isra'ila a ranar Alhamis har zuwa tsawon sa'o'i biyar domin amsa kiran MDD, in ji wani jami'in da bai bukaci a ambata sunansa ba, ya bayyana cewa, Hamas za ta mai da martani ga duk wasu hare-haren Isra'ila a zirin Gaza idan har Isra'ila ta sabawa wannan lokaci na dakatar da karar makamai.
A ranar Laraba da yamma, rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ta bayyana cewa, za ta giramama yarjejeniyar tsagaita bude wuta domin domin aikin jin kai daga karfe 10 na safe zuwa karfe uku na yamma bisa agogon wurin a tattaunawarta tare da MDD, amma ta nuna cewa, idan Hamas ta harba rokoki zuwa Isra'ila a tsawon wannan lokaci, to Isra'ila ita ma za ta mai da martani. (Maman Ada)