Kungiyar Hamas ta sanar da Masar cewa, ba za ta amincewa da tayinta ba na tsagaita bude wuta tsakanin mayakanta dake zirin Gaza da Isra'ila. Sami Abou Zouhri, kakakin kungiyar Hamas a Gaza ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, kungiyarsa ta sanar da Masar a hukunce cewa, ba za ta amince da tayin ba, ko da yake jami'in bai ba da wani karin haske ba.
A gefe guda kuma ana cigaba da gudanar da kokari daga wasu bangarori daban daban tun yau da 'yan kwanaki domin ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da mayakan Hamas dake Gaza.
Wasu rahotonni sun shaida cewa, shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ya je Masar domin tattauna batun tsagaita bude wuta a zirin Gaza. Haka kuma wasu kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, mista Abbas ka iyar ganawa a birnin Alkahira da manyan jami'an Hamas, Khaled Mechaal da Moussa Abou Marzouk domin tattauna tayin Masar na tsagaita bude wuta a Gaza. (Maman Ada)