in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hamas ta amince da kudurin tsagaita wuce na sa'o'i 24
2014-07-27 20:48:49 cri
Kungiyar Hamas ta Falasdinu ta bayyana amincewarta da kudurin dakatar da bude wuta tsahon sa'o'i 24, da nufin ba da damar shigar da kayayyakin agajin jin kai zirin Gaza.

Ta wani sakon wayar salula da ya aike ga manema labaru a Lahadin nan, kakakin kungiyar Sami Abu Zuhri, ya ce Hamas ta amince da wannan kuduri ne, bisa la'akari da ta yi da bukatun al'umma, da kuma kudurin MDD na shiga tsakani, a musayar wutar da Falasdinawan ke yi da tsagin Isra'ila.

Rahotannin baya bayan nan dai sun nuna cewa, kudurin tsagaita bude wutar zai fara aiki ne tun da karfe 2 na yammacin Lahadin nan bisa agogin wurin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China