A ranar talatan nan aka amince ma Kosovo data aika da tawagarta mai zaman kanshi a matsayin mamba na wasannin Olympic na shekara ta 2016 a Rio de Jameiro bayan da kwamitin wasannin Olympics na duniya wato IOC ya tabbatar da kasar dake yankin Balkan a matsayin cikakkiyar mamba.
Majalisar zartarwar kwamitin wasannin na duniya ta amince da wannan bukatar da aka mika tun a watan Oktoban, Kosovo dai ta sami 'yan cin kanta ne daga kasar Serbia a shekarar ta 2008 ta zama kasa ta 205 da kwamitin wasannin olympic din na duniya ya amince da wakilcinta.