Philémon Yang ya ziyarci ganuwar yaki da igiyar ruwa, da yankin ajiye akwatuna, da kuma tashar jirgin ruwa da za a kammala su nan ba da dadewa ba. Shugaban reshen kamfanin CHEC a Kamaru, Xu Huajiang ya gabatar da fasali, da ayyukan da ake yi, da hanyoyin da ake bi ga Philémon da 'yan rakiyarsa.
Xu ya ce, ma'aikatan kamfanin CHEC da na Kamaru suna iyakacin kokarinsu, tare da shawa kan wahalhalu da dama, a kokarin tabbatar da kammala wannan tashar jirgin ruwa mai tsayi ta farko a tsakiyar nahiyar Afirka cikin lokaci mai inganci.
A nasa bangare, Firaminista Philémon ya bayyana wa 'yan jaridu bayan kammala ziyararsa cewa, wannan tashar jirgin ruwan tana da muhimmanci sosai wajen samun ci gaban kasar Kamaru a nan gaba, don haka gwamnatin kasar Kamaru ta amince da sauri da ingancin wannan aiki kwarai, sannan kokarin bangarorin daban daban ya burge su sosai.
Baki daya an kebe kudi kimanin dala miliyan 497 wajen kafa wannan tashar jirgin ruwa mai tsayi a zagaye na farko. An aza tubali a watan Oktoban shekarar 2011, aikin dake da wa'adin watanni 36 za a kammala shi a badi.(Fatima)