in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa ne a cimma daidaito game da batun sauyin yanayi
2014-06-29 16:35:47 cri
Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya ce mai yiwuwa ne kasashen duniya su kai ga cimma matsaya guda game da batun daukar matakan shawo kan sauyin yanayi nan da karshen shekarar 2015 mai zuwa.

Mr. Ban wanda ya bayyana hakan a birnin Nairobin kasar Kenya, ya kara da cewa, illolin da sauyin yanayi ke haifarwa ga samar da abinci na da mummunan tasiri, musamman ga kasashen dake nahiyar Afirka da sauran kasashen masu tasowa.

Don gane da hakan ne babban magatakardar MDDr ya bukaci shuwagabannin kasashen duniya da su dauki matakan da suka wajaba, domin kaucewa illolin da ake hasashe, tare da bada damar samar da isasshen abinci ga dunbin al'ummar duniya.

Mr. Ban, wanda yayin ziyarar da ya kammala jiya Asabar a kasar ta Kenya, ya jagoranci rufe babban taron kiyaye muhalli na MDD, ya kuma bayyana matukar damuwa game da karuwar ayyukan ta'addanci a yankunan dake yammaci da gabashin nahiyar Afirka. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China