in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin ruwan kasar Sin zai taimakawa wajen neman akwatin nadar bayanan jirgin saman da ya yi hadari
2015-01-05 15:17:12 cri

Yau Litinin 5 ga wata da karfe 10 na safe, ma'aikatar harkokin sufuri da zirga-zirga ta kasar Sin ta aika da jirgin ruwan ba da agaji mai suna Nanhai 101 zuwa yankin tekun Indonesia daga birnin Haikou na kasar Sin domin amsa bukatar kasar Indonesia a fannin ba da taimako wajen neman akwatin nadar bayanan jirgin sama mai lambar QZ8501 na kamfanin AirAsian da ya fada cikin ruwan tekun Java.

Bayan abkuwar hadarin, cibiyar ba da agaji a teku a karkashin shugabancin ma'aikatar harkokin sufuri da zirga-zirga ta kasar Sin da cibiyar ba da agaji a teku ta Indonesia sun tuntubi juna cikin lokaci game da wannan lamarin. An kiyasta cewa, a ranar 9 ga wata jirgin ruwan ba da agaji mai suna Nanhai 101 zai isa yankin tekun inda zai fara taimakawa wajen neman akwatin. Ban da haka kuma, ma'aikatar harkokin sufuri da zirga-zirga ta kasar Sin ta umurci wani jirgin ruwan ba da agaji na daban da ya share fage yadda ya kamata.

An labarta cewa, wata kungiyar masana daga kwalejin nazarin kimiyyar zirga-zirga kan teku dake birnin Tianjin ta riga ta tashi daga Tianjin tare da wasu na'urorin bincike, zuwa birnin Sanya, inda kuma za su yi amfani da jirgin ruwan ba da agaji mai suna Nanhai 101 domin neman akwatin nadar bayanan wannan jirgin sama. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China