Shugaban cibiyar bada ceto ta kasar Indonesia ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a daren ranar 4 ga wata cewa, ya zuwa yanzu, an gano gawawwakin mutane 34 da suka mutu a sakamakon hadarin, kuma aka kai su zuwa asibitin 'yan sanda dake Surabaya don tantance da su. Kuma bangaren 'yan sanda na jihar gabashin Java na kasar Indonesia ya sanar a gun taron manema labaru da aka gudanar a birnin Surabaya a wannan rana cewa, an samu tantance asalin gawawwakin mutane 9 da aka gano.
A halin yanzu dai, ba tabbatar da gano dalilin abkuwar wannan hadarin ba, amma a ganin rahoton bincike da hukumar kula da harkokin yanayi ta kasar Indonesia ta bayar, watakila yanayi shi ne dalilin hadarin. Rahoton ya bayyana cewa, mai yiwuwa ne jirgin saman ya gamu da kankara yayin da yake kan hanya, wanda ta lalata injin jirgin saman. Bisa binciken yanayi, ana tsammanin wannan ne ya haddasa hadarin, amma kuma duk haka ba shi ne rahoton karshe ba game da dalilin wannan hadari, domin har yanzu ba'a gano akwatunan adana bayanai na jirgin saman ba. (Zainab)