Jirgin saman mai lamba QZ8501 wanda ya tashi ne daga Indonesia a kan hanyarsa ta zuwa Singapore. Amma sai jirgin ya bace bayan minti 42 da tashinsa a ranar Lahadi. Daga baya sai aka gano jirgin ya yi hatsari.
A yau Alhamis an kai wasu gawawwaki domin tantance su zuwa wani asibitin 'yan sanda na Surabaya, hekwatar lardin Java dake yankin gabashin kasar Indonesia.
Kwamandan rundunar sojoji masu bincike da gano gawawwakin wadanda suka yi hadarin a jirgin, Mr Eko Wiratmoko ya ce rashin kyaun yanayi ya kawo tsaiko a wurin binciken.
Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya mika ta'aziyarsa ga iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su.
Wata sanarwar da ta fito daga kakakin magatakardan MDD ta mika godiya ga gwamnatocin da suka kawo dauki domin kaddamar da bincike na gano jirgin bayan da ya bace. (Suwaiba)