Daya daga cikin tarkacen da aka gano ya kai tsawon mita 18 da 5.4. Amma, har yanzu ba a samu akwatin nadar bayanan jirgin ba. Abin da aka mayar da hankali yanzu shi ne nema da kuma tsamo gawawwakin mutanen da suka mutu sakamakon lamarin.
Haka zalika a ranar 3 ga wata, wani jami'in ma'aikatar sufuri ta kasar Indonesiya ya bayyana cewa, ma'aikatarsa za ta binciki duk tsarin zirga-zirga na kamfanin AirAsian, kuma za a dakatar da hanyar Surabaya na kasar Indonesiya zuwa kasar Singapore.
Mukaddashin babban sashen sufurin jiragen sama na ma'aikatar sufuri ta kasar Indonesiya ya bayyana a wannan rana cewa, bisa binciken da aka yi, an gano cewa, jirgin sama mai lambar QZ8501 na kamfanin AirAsian da ya fada "ba shi da iznin bin hanyar Surabaya zuwa Singapore a wannan rana". Bayan haka kuma ya ce, za a dakatar da zirga-zirgar jirage a wannan hanyar har zuwa lokacin da aka kammala bincike. (Bilkisu)