An samu nasara a aikin laluben jirgin saman kamfanin AirAsian nan da ya bace a ranar Lahadi. Inda mahukuntan kasar Indonesia suka bayyana cewa, an gano tarkacen jirgin, tare da wasu gawawwakin mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin.
Cibiyar gudanar da aikin ceto ta kasar Indonesiya ta sanar da wannan ci gaba. Yanzu dai jiragen ruwa, da jiragen sama masu yawa na kan hanyar su zuwa yankin da hadarin ya auku, domin ci gaba da ayyukan ceto.
Wannan jirgin fasinja mallakar kamfanin zirga-zirga na AirAsia mai lamba QZ8501, ya bace ne dauke da fasinjoji 155, da kuma ma'aikata 7, an kuma dai na jin duriyarsa ne daga cibiyar ba da umurnin jiragen sama, bayan tashinsa daga Indonesiya zuwa kasar Singapore.
Yanzu haka dai jiragen ruwa 30, da na sama 21 daga kasashen Indonesia, da Malaysia, da Sigapore da Australia ne ke aikin ceton jirgin a yankin teku.
Kaza lika mahukuntan kasar Sigapore, da wasu karin kasashe sun bayyana aniyar kara yawan jiragen ruwa, domin shiga aikin neman tarkacen jirgin saman.
Sakamakon cimma daidaito da gwamnatin kasar Indonesia, ita ma kasar Sin ta kuduri aniyar tura jiragen sama, da na ruwa, domin shiga wannan aiki. Tuni kuma jirgin ruwan soja na kasar ta Sin mai suna Huangshan, ya kama hanya zuwa yankin tekun da jirgin saman ya fadi.
Babban jami'in zartaswa na kamfanin AirAsia Tony Fernandes, ya bayyana matukar kaduwa game da aukuwar wannan hadari. Har wa yau ya jajantawa iyalan wadanda hadarin ya ritsa da su a madadin kamfanin. Yana mai cewa, aukuwar wannan hadari ta jefa kamfanin cikin mawuyacin hali. (Zainab)