Yanzu haka dai jirgin ruwan sojin kasar Sin guda daya dake sintiri a tekun kudu ya riga ya kama hanya zuwa yankin tekun da jirgin saman ya bace, kana jiragen saman sojan kasar ta Sin, na tattaunawa da tsara hanyoyin aiki tare da na sauran kasashen da abin ya shafa.
A daya bagaren kuma, kakakin sojin saman kasar Sin Liang Yang, ya ce an umarci jirgin ruwa na Huangshan, da ya canja aikin sintiri a tekun kudu, zuwa aikin neman jirgin saman da ya bace.
Haka zalika an shirya jiragen sama, da kayayyakin aiki, da na'urorin gudanar da ayyukan ceto na kasar Sin, domin shiga yankin tekun da jirgin saman ya bace, da burin gudanar da aikin ceto. (Zainab)