Wannan ne karo na farko da shugaba Xi Jinping zai kai ziyara a yankin Macau bayan da ya hau kujerar shugabancin kasar Sin.
Bisa labarin da aka bayar an ce, wannan ziyara da shugaba Xi Jinping zai kai a yankin Macau na janyo hankali sosai a yankin, bangarori daban daban suna ganin cewa, wannan ziyarar Xi Jinping ta sheda kulawa da goyon baya da gwamnatin kasar Sin ta nuna wa yankin Macau. Sa'an nan suna maraba da zuwan shugaba Xi Jinping. Don haka, gwamantin yankin Macau za ta shirya jerin bukukuwa don taya murnar cika shekaru 15 da komawar yankin a kasar Sin. (Zainab)