Wu Xinxiong ya bayyana a gun taron ayyukan makamashi na kasar Sin da aka gudanar a wannan rana cewa, mataki na farko shi ne a tsara shirin raya sha'anin makamashi cikin matsakaici da dogon lokaci, da kuma tattauna da tabbatar da burin samar da makamashi a shekarar 2030.
Na biyu, a sa kaimi ga yin kwaskwarima kan aikin yin amfani da makamashi don inganta aikin samar da makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhallin halittu.
Na uku, a kara yin kwaskwarima kan aikin samar da makamashi, da kyautata tsarin makamashi. Za a himmatu wajen raya aikin samar da wutar lantarki da karfin ruwa, iska da kuma hasken rana, gami da raya aikin samar da wutar lantarki ta amfani da karfin nukiliya cikin lumana.
Na hudu, a kara inganta fasahohin samar da makamashi, da dora muhimmanci kan kirkiro manyan fasahohi na zamani.
Na biyar, a kirkiro sabon tsarin samar da makamashi, da yin gyare-gyare a fannonin samar da wutar lantarki, iskar gas, farashin makamashi da dai sauransu.
Na shida, a mai da hankali kan tsaron makamashi, da kara karfin takara a duniya, baya ga inganta hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa a wannan fanni, a kokarin kiyaye tsaron makamashi yayin da ake bude kofa a wannan fanni.
Na karshe shi ne, a raya hukumar kula da harkokin makamashi ta kasar Sin yadda ya kamata, ta yadda za ta gudanar da ayyukanta bisa doka. (Zainab)