Kasar Najeriya ta bukaci a ranar Talata masu zuba jarin kasashen waje da su taimaka a bangaren kimiyyar sabon makamashi da zai taimaka wajen tsimin makamashi domin warware karancin gine-gine a wannan fanni.
Ministan makamashin Najeriya, Chinedu Nebo ya yi wannan kiran a yayin bude dandalin kasa da kasa kan makamashi karo na uku a birnin Lagos. Mista Nebo ya baiwa masu zuba jari na kasashen waje kwarin gwiwa da su kara zamansu a Najeriya.
Muna ba ku kwarin gwiwa wajen cigaba kan abin da kuke yi da kuma yadda za ku yi na kara zamanku a cikin wannan kasa, in ji mista Nebo.
Haka ya kuma ba da tabbacin cewa, gwamnati za ta yi kokari domin kafa wani yanayi mai kyau ga masu zuba jari domin kyautata matsalar makamashin kasar. Dandalin karo na uku ya kasance wata hanya da ke baiwa masu baje koli damar gabatar da kayayyakinsu a bangarorin sarrafawa, aikewa da rarraba wutar lantarki, samar da hasken wuta da sabbin makamashi, makamashin nukuliya da bangarorin ruwa. Haka kuma haduwar ta kwanaki uku ta janyo kusan kamfanoni dari da suka fito daga kasashen Italiya, Sin, Faransa, Rasha, Turkiya, Jamus da sauransu. Najeriya na daya daga cikin kasashen dake da ma'aunin samar da wutar lantarki a kowane gida ya kasance mafi kankanta a nahiyar Afrika, kuma rabin al'ummar daga cikin miliyan 160 ba su da wutar lantarki. (Maman Ada)