in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen tsakiyar Afirka 10 sun zartas da takardar amfani da makamashi mai tsabta
2014-10-21 10:59:01 cri

Ministocin makamashin kasashe 10 mambobin CEMAC wato tarayyar tattalin arziki da kudi ta tsakiyar Afirka da CEEAC wato tarayyar tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afirka sun yi taro a Yaounde, babban birnin kasar Kamaru a ranar 18 ga wata, inda suka duba kuma suka zartas da takardar game da neman samun hidimar makamashi mai tsabta da manufofin yankin wajen ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma.

An zartas da wannan takardar ne a karkashin goyon bayan hukumar UNDP ta MDD a fannin fasaha da kudi, makasudin aikin shi ne domin kara amfani da karfi wajen samar da makamashi, ta yadda za'a samar da isasshen lantarki a yankin, tare da ciyar da tattalin arziki gaba yadda ya kamata.

Domin cimma burin, ana bukatar kudi da yawa, wato idan ana son samar da lantarki a wurare kusan kashi 54 bisa dari a yankin tsakiyar Afirka nan da shekarar 2030, to ana bukatar dalar Amurka biliyan 14.8. Kuma bisa kididdigar da aka yi, yanzu jama'ar yankin kusan kashi 15 bisa dari ne kawai suke amfani da makamashi mai tsabta. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China