in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambiya za ta sakin bangaren makamashinta kasuwa
2014-11-27 14:13:33 cri

Gwamnatin Zambiya tana shirin sake duba ayar dokar dake shafar bangaren makamashin kasar domin kara bude kofa ga masu zuba jarin bangaren masu zaman kansu, in ji jaridar Times of Zambia a ranar Laraba. Charles Zulu, sakataren din din din na ma'aikatar ma'adanai, makamashi da ruwa, ya bayyana hakan cewa, gwamnatin na da shirin sake duba dokokin dake daidai harkokin wutar lantarki da makamashi, da zummar saki kasuwa da kuma ba da damar kulawa da bangaren bisa 'yanci.

A cewarsa, baiwa kamfanonin gwamnati damar shiga kasuwa da samun yarin waje zai samar da matakin kafa wani yanayi mai kyau da zai taimaka wajen kara samun zuba jarin masu zaman kansu a cikin bangaren. Haka kuma ya jaddada cewa, ya kamat a kara bunkasa zuba jarin masu zaman kansu domin kara samar da wutar lantarki ga jama'ar kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China