in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukunin binciken wadanda suka kamu da cutar Ebola da kasar Sin ta tura kasar Saliyo ya gudanar da ayyuka yadda ya kamata
2014-11-24 10:29:47 cri
Bisa labarin da rukuni na biyu na binciken wadanda suka kamu da cutar Ebola da cibiyar rigakafi da yaki da cututtuka ta kasar Sin ta tura zuwa kasar Saliyo ya bayar a ranar 23 ga wata, an ce, an gudanar da ayyukan gwaji da cibiyar sa ido kan wadanda suka kamu da cutar yadda ya kamata, kana rukuni na farko na bincike kan masu kamu da cutar ya mika ayyuka ga rukuni na biyu.

Rahotanni na cewa, ya zuwa ranar 22 ga wata, cibiyar sa ido kan wadanda suka kamu da cutar Ebola dake asibitin sada zumunta na Sin da Saliyo ta karbi mutane 303 da ake zaton sun kamu da cutar, guda 166 a cikinsu ne aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola.

A ranar 15 ga wata ne rukuni na biyu na bincike kan cutar Ebola na cibiyar rigakafi da yaki da cututtuka ta kasar Sin ta tura ya isa kasar Saliyo don maye gurbin rukuni na farko. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China