Wasu rahotanni da wasu hukumomi guda biyu na MDD wato hukumar samar da abinci da aikin gona ta FAO da shirin abincin duniya WFP suka gabatar na nuni da cewar, kididdigar mutanen da ke fuskantar karancin abinci saboda cutar Ebola mai saurin kashe jama'a a kasashen Guinea, Liberia da Saliyo a halin yanzu za su iya kaiwa kusan miliyan daya nan da zuwa watan Maris na shekara ta 2015, idan har ba'a dauki matakan kariya ba na abincin da aka shuka da kuma dabbobin da ake kiwo.
Rahotannin sun ce, cutar Ebola ta haifar da matsaloli da suka yi tasiri a wadannan kasashen wadanda dama suna fama da matsalar karancin abinci.
Rahotannin sun ce, lamarin ya ta'azzara saboda wasu matakan da aka dauka saboda haramta yaduwar cutar Ebola sun haifar da karancin abinci kuma hakan na barazana ga rayuwar jama'a. (Suwaiba)