Shugaba Obama ya saka hannu a kan dokar ne ba tare da wani bata lokaci ba bayan amincewar da majalisun kasar guda biyu suka yi a ranar laraba, Da yake jawabi jim kadan da amincewar 'yan majalisar dattawan ya ce da zaran takardar dokar ta iso kan teburin shi,za'a fara hada hadar bude ma'aikatun gwamnati nan take ba tare da bata lokaci ba,ya mika godiyar sa ga 'yan jam'iyyar demokrats da na republicans game da cimma yarjejeniyar da za'a kawo karshen rufe ma'aikatun gwamnati tare da kara adadin yawan kudin da kasar zata iya ciwo wa bashi.
Yace da fatan irin haka ba zai sake shiga wani tsaka mai wuya ba don haka ya kamata a kara samun fasahar fitar da kasar daga wani halin na ni 'yasu. Jim kadan da Shugaba Obaman ya saka hannu kan dokar,Direktan tsarin kudin kashewa na fadar gwamnati a white house Slyvia Mathews Burwell ta fitar da umurni ga ma'aikatan ta cewa gwamnati za ta yi iyakacin kokarinta wajen yin abubuwan da suka kamata don ganin komai ya tafi dai dai. (Fatimah Jibril)