Wannan dai taro na masu ruwa da tsaki ya biyo bayan rufe wasu daga cikin ofisoshin diplomasiyyar kasar ta Amurka da aka ayyana gudanarwa a ranar Lahadin nan.
Wata sanarwar da fadar ta White House ta fitar ta bayyana cewa, babbar mai ba da shawara ta fuskar tsaro Susan Rice ce ta jagoranci taron, wanda ya samu halartar manyan mataimaka ga shugaba Barack Obama, da manyan sakatarori, da kuma shuwagabannin hukumomin tsaron cikin gida da waje. Sanarwar ta ce, makasudin taron na ranar Asabar shi ne sake nazartar matakan da aka rigaya aka dauka, tare da tattauna matakan da suka dace a dauka a nan gaba.
A cewar waccan sanarwa, duba da muhimmancin da wannan batu ke da shi, babbar mataimakiya ga shugaban kasa kan harkokin tsaro, da yaki da ta'addanci Lisa Monaco ta gana da sassan hukumomin tsaro daban daban cikin satin da ya gabata, kuma tuni aka yi wa shugaba Obama cikakken bayanin halin da ake ciki.
A wani ci gaban kuma a yau Lahadi ne kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus suka bayyana aniyarsu ta rufe nasu ofisoshin diplomasiyya dake kasar Yemen tsawon a kalla makwanni biyu, yayin da ita ma kasar Canada ta bayyana rufe ofishinta dake kasar Bangaladesh. Ana dai ganin daukar wannan mataki na da nasaba da ayyana rufe ofisoshin diplomasiyyar Amurka da aka yi a kasashen musulmi daban daban, sakamakon bayanan sirrin da hukumomin tsaron kasar suka ce sun bankado. (Saminu)