in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Amurka ta amince da fidda wasu bayanan kan shirin lura da layukan wayoyin fararen hula.
2013-08-01 12:41:43 cri
Shugaba Barack Obama na Amurka ya amince da gabatarwa majalissar dattijan kasar wasu kundin bayanai 3, masu kunshe da shirye-shiryen sirri na hukumar tsaron kasar, ciki hadda na shirin tattara bayanai kan wayoyin da fararen hula ke yi.

Rahotanni dai sun bayyana cewa shirin sanya ido tare da tara bayanai kan wayoyin tarho da fafaren hula ke yi a kasar, na cikin sirrikan hukumar tsaron Amurkan da mai tonon sililin nan Edward Snowden ya fallasa a cikin watan Yunin da ya gabata. Lamarin da ya haifar da tafka mahawara mai tsanani, tsakanin tsagin masu kare halascin yin hakan, da masu adawa da shirin.

A cewar babban daraktan hukumar harkokin tsaron kasar ta Amurka James Clapper, gabatar da wadannan bayanai dake kunshe da cikakkun bayanai, don gane da shirin da ya jawo takaddama na da muhimmanci, ya kuma dace da bukatun al'umma na sanin hakikanin yadda al'amura ke gudana.

Baya ga batun tattara bayanai kan wayoyin fararen hula, akwai kuma bayanai kan wata doka mai dauke da amincewar kotu, wadda ta baiwa jami'an hukumar tsaron kasar damar neman wani kamfani da ba a ambaci sunan sa ba, ya gabatar da dukkanin bayanai da suka shafi lambobi, da tsawon lokacin da abokan huldarsa suke shafewa suna waya a kowace rana. Koda yake dai wannan doka bata hada da sauraron tattaunawar da ake yi a wayoyin ba.

Har ila yau akwai wata wasika da aka rubuta cikin shekarar 2009, wadda ke kunshe da bayanai, masu jaddada muhimmancin dokar fadada ayyukan tsaro da suka shafi bankada sirrikan fararen hula, da nufin dakile yiwuwar aukuwar ayyukan ta'addanci a dukkanin fadin kasar.

A zaman majalissar na ranar Laraba, da dama daga mambobinta sun bayyana bukatar duba na tsanaki kan wannan batu, bisa la'akari da irin sarkakiya da harkar tsaron kasa ke tattare da ita. Don gane da wannan batu Sanata Patrick Leahy, dake matsayin shugaban kwamitin shari'a a majalissar yace dole ne a sanya ido, tare da tabbatar da kyakkyawan amfani da irin dokokin da majalissar ke amincewa hukumomin tsaro amfani da su. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China