in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da matsa kaimi ga batun cimma yarjejeniyar nukiliyar Iran
2014-11-22 17:01:45 cri
Gwamnatin kasar Amurka ta bayyana cewa, a halin yanzu kasar Iran da kasashen shida da batun nukiliyar ta Iran ya shafa, na ci gaba da tattaunawa a birnin Vienne na kasar Austria, domin zakulo hanyar da za ta kaiga warware babban sabanin dake tsakanin bangarorin da batun ya shafa.

Amurka ta ce ana fatan kulla wata yarjejeniya bisa dukkan fannoni, kan nukiliyar kasar ta Iran, kafin ranar 24 ga watan nan da muke ciki, wanda shi ne karshen wa'adin shawarwarin da ba a fatan tsawaitawa.

Rahotannin baya bayan nan dai na cewa a halin yanzu, babban sabanin dake tsakanin Iran, da sauran kasashe shida da batun nukiliyarta ya shafa sun hada da girman shirin harkokin nukiliyar Iran din, musamman ma yawan wasu na'urorin sarrafa nukiliyar kasar, da kuma batun kawar da takunkumin da aka kakaba mata.

Sai dai galibin kafofin watsa labarai na ganin cewa, bangarorin da wannan batu ya shafa ba za su iya kulla wata yarjejeniya kafin ranar 24 ga wata ba, kuma mai iyuwa ne a kai ga sake tsawaita shawarwarin da aka fara.

A baya ma dai an yi fatan kammala shawarwarin ne tun ranar 20 ga watan Yulin da ya gabata, sai dai rashin samun nasarar hakan ne ya sanya sake daga wannan kuduri zuwa ranar 24 ga watan nan na Nuwamba, tattaunawar da aka fara a ranar 18 ga wata a birnin na Vienna. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China