in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kare tattaunawa tsakanin bangarori uku akan nukiliuyar Iran ba da wani cigaba sosai ba
2014-11-11 17:01:07 cri
An kawo karshen tattaunawa tsakanin bangarorin Amurka da kungiyar tarayyara Turai da ita kan ta kasar Iran ba tare da samun wani cigaban a zo a gani ba, a ranar litinin din nan 10 ga wata.

Taron na kwanaki biyu da ya samu halartar Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ,Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif da kuma mai bada shawarar ga kungiyar tarayyar Turai Catherine Ashton yazo ne makonni biyu kafin wa'adin 24 ga watan Nuwambabn nan na cimma matsaya akan batun nukuliyar ta kasar Iran. Takunkumin kasashen yammaci akan Iran da kuma arzikin kasar a ma'adinan Uranium sun zama manyan batutuwa biyu a tattaunawar mai karfi.

Bayan taron, wani jami'in kasar Iran ya bayyana ma manema labarai cewa ba a samu wani cigaban azo a gani ba sakamakon tattaunawa kuma har yanzu akwai tazara a kan manyan batutuwan. Tattaunawar na daga cikin shirin daidaita batun da EU ke jagoranta tsakanin kasar ta Iran da kasashe da ake kira P5+1 da suka hada da Ingila, Sin,Faransa, Rasha da Amurka sannan kuma da Jamus.

Iran da wadannan kasashen zasu sake sabon tattaunawa a kan batun nukiliyar a ranar talata a Birnin Muscat,kamar yadda wasu jami'an kasar Oman suka bayyana. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China