Dangane da lamarin, a yau Laraba 19 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yayin taron manema labaran da aka saba yi cewa, kasar Sin tana son ci gaba da halartar shawarwari kan wannan batun, don dukufa wajen ganin an cimma wata cikakkiyar yarjejeniya da ta dace da moriyar juna bisa lokacin da aka tsara.
Kasar Sin na ganin cewa, abin da ya fi muhimmanci a halin yanzu shi ne, ya kamata bangarori daban daban da abin ya shafa su tsaya tsayin daka kan batutuwan da suka riga suka cimma matsayi daya a kai, su kuma warware sabanin dake tsakaninsu yadda ya kamata bisa ka'idar adalci, ta yadda za su bullo wata hanyar da ta dace na warware manyan matsalolin dake janyo hankulan bangarorin da abin ya shafa bisa lokacin da aka tsara. (Maryam)