A yau Litinin ne yayin taron manema labaran da aka saba yi kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasa ta Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Sin ta yi allah wadai da harin da aka kai a kasar Pakistan, kuma Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen nuna goyon baya ga kokarin da gwamnati da jama'ar kasar Pakistan suke yi na kiyaye zaman karko da tsaron kasar.
Rahotanni sun bayyana cewa, a jiya Lahadi 2 ga wata ne, aka kai wasu munanan harin boma-bomai a garin Wagah dake kusa da birnin Lahore na kasar Pakistan, wanda ya haddasa mutuwar mutane sama da 60, yayin da wasu da dama suka jikkata. (Maryam)