in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ita ce kasa ta farko da ta samar da gudummawa ga kasar Pakistan
2013-09-26 20:35:20 cri
Bisa labarin da ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin ta bayar, an ce, Sin ta tsai da kudurin bada taimakon kudi dala miliyan 1.5 da kayayyakin jin kai da yawansu ya kai Yuan miliyan 30 ga gwamnatin kasar Pakistan don taimakawa mutane masu fama da bala'in girgizar kasar da ta abku a kasar.

Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Pakistan ya bayyana cewa, kasar Pakistan ta nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin domin gudummawar da ta bayar cikin lokaci, kana ya ce, kasar Sin ita ce kasa ta farko da ta samar da gudummawa ga kasar Pakistan. Wannan ya bayyana irin zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, kuma taimakon da Sin ta bayar zai taimakawa jama'ar kasar wajen sake gina kasar cikin hanzari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China