Shahararrun jaridun kasar da suka hada da Daily News, Guardian, da Citizens sun fidda wasu bayanai dake nuna cewa, kamfanin fasahohin jiragen sama na kasar Sin, ya samu nasarar kafa cibiyar farko ta fasahohin jiragen sama a birnin Dar es Salaam, domin samarwa nahiyar Afirka jiragen sama da fasahohin sadarwa masu inganci, da kuma kayayyakin jiragen sama da dai sauransu.
Kaza lika kamfanin zai yi shawarwari tare da kamfanin jiragen sama na kasar Tanzania game da kafa kamfanin hadin gwiwa, da kuma samar da jiragen sama gare shi.
Labarin ya tsamo jawabin wakilin ma'aikatar harkokin sufuri ta kasar Tanzania wanda ya halarci bikin na cewa, wannan cibiya tana daya daga cikin shirye-shiryen hadin gwiwa da shugaban kasar Tanzania ya daddale, a yayin ziyararsa a kasar Sin, wadda kuma ta nuna makoma mai kyau ga kasashen biyu a wannan fanni.
Kamfanin fasahohin jiragen sama na kasar Sin ya kaddamar da wannan cibiya ne dai kafin ya kafa kamfanin hadin gwiwar samar da jiragen sama ga kasar ta Tanzania, matakin da ya nuna sahihiyar niyarsa a fannin hadin gwiwa tare da kasar Tanzania, matakin da ya sanya kasar Tanzania jinjinawa wannan kamfani. (Zainab)