Hukumar adana kayayyakin tarihi ta kasar Sin da ma'aikatar kula da harkokin albarkatun halittu da yawon bude ido ta Tanzania da ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Tanzania ne suka shirya wannan biki cikin hadin gwiwa.
A yayin bikin kaddamar da wannan nune-nune, Mr. Mabura, shugaban gidan adana da nune-nunen kayayyakin tarihi na kasar Tanzania ya nuna yabo sosai ga kayayyakin tarihi da ake nunawa. Ya bayyana cewa, wadannan kayayyakin tarihi sun bayyana yadda aka fara kafa aminci tsakanin kasashen Sin da Tanzania a lokacin da aka bude wannan hanyar siliki ta ruwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. (Sanusi Chen)