Daga nan sai ya yabawa Sin bisa gudummawar da take baiwa kasashen Afirka ba tare da gindaya wani sharadi ba. Baya ga goyon bayanta gare su wajen yaki da mulkin mallaka, da samun bunkasuwar tattalin arziki. Kana ya ce, kasar Sin ta kiyaye sada zumunta tsakaninta da kasashen Afirka, yayin da take samun babbar nasara kan bunkasuwar tattalin arziki da dagawar matsayinta a duniya. A ganinsa, wannan zumunta na wanzuwa bisa tushen girmama juna da cimma moriyar juna.
A daya hannun, Mr. Sanga ya bayyana gagarumin ci gaban da kasar Sin ta samu sakamakon aiwatar da manufar bude kofa da yin kwaskwarima a matsayin sabuwar dama ga kasashen Afirka, kana ya bayyana cewa idan har kasashen Afirka na son samun bunkasuwa, to kamata ya yi su kara koyi daga fasahohi daga kasar Sin ke bi.
Kaza lika ya yi imani da cewa, a matsayin amintacciyar abokiyar kasashen Afirka, kasar Sin za ta iya taimakawa kasashen na Afirka wajen samun 'yancin kai a fannin siyasa, da samun bunkasuwar tattalin arziki na kashin kan su. (Zainab)