Tattalin arzikin kasar Libya dai na dogaro da man fetur inda kasar take samun kudaden shiga na sama da kashi 95 bisa 100 na man fetur din da take fitowar zuwa kasashen ketare.
Tun ranar 13 ga watan Yuli, ake ci gaba da samun ricike-rikice tsakanin kungiyoyin biyu a babban birnin Tripoli da birnin Banghazi da wasu biranen kasar, haka kuma sakamakon rikice-rikicen, gwamnatin wucin gadi da sabuwar majalisar dokokin kasa dake wakiltar jama'ar kasar sun kaura zuwa karamin birnin Tobruk dake gabashin kasar. Bugu da kari, kungiyar tsagerun dake goyon bayan addini, ta taimaka wa majalisar dokokin kasar da aka riga kawo karshen wa'adinta farfado da mulkinta, bayan da kungiyar ta mamaye birnin Tripoli, ta kuma kafa wata sabuwar gwamantin tsaron kasa. Lamarin da ya sa, a halin yanzu, akwai gwamnatoci biyu da kuma majalisun dokokin biyu dake kasancewa a kasar Libya. (Maryam)