Wadanda suka sheda da idon su sun bayyana cewa, motocin soja mai dauke da makamaya sun kutsa kai cikin birnin, abin da ya sa su kuma mayakan kungiyar masu kaifin addini suka fara kafa mazaunar su a lokacin da motocin sulken suketa harbi ta ko ina wanda hakan ya sa garin yin shiru in ban da kara luguden wuta dake tashi.
Harin ya zo ne awanni bayan da Janar Haftar ya yi jawabi ta kafar talabijin mallakar magoya bayan sa, yana mai bayanin cewa, sojojin gwamnati za su kore kungiyar masu kaifin addini daga birnin. A don haka ya yi kira ga al'umma da su tashi tsaye don yakan 'yan ta'addan. (Fatimah Jibri)