Rahotanni sun bayyana cewa daga ranar 15 ga watan Oktoba ya zuwa wannan lokaci, dakarun kungiyoyin 'yan ba ruwanmu masu goyon bayan gwamnatin wucin gadi ta kasar Libya, sun yi gumurzu da nufin kwace ikon mallakar birnin Banghazi, sun kuma fafata da dakarun fararen hula na kungiyar masu kishin addini.
Wani jami'in asibiti a birnin na Banghazi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu mutane a kalla 450 ne suka rasu sakamakon wadannan rikice-rikicen, ciki har da mayaka da kuma fararen hula.
Jami'in ya kara da cewa, ana samun alkaluman yawan gawawwakin wadanda suka rasa rayukansu daga asibitoci da dama a birnin na Banghazi. Sai dai ya ce da yake dakarun kungiyar masu kishin addini ba sa kai mambobinsu da suka rasu, ko suka samu raunuka zuwa asibiti, yawan mutanen da suka mutu a sakamakon rikice-rikicen, a hakika ya zarce mutum 450. (Zainab)