in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen Libya da kasashen dake makwabataka da ita sun yi kira da a kawo karshen rikicin kasar
2014-12-05 10:44:26 cri
An gudanar da taron ministocin harkokin wajen kasar Libya da kasashen dake makwabtaka da ita a karo na 5 a birnin Khurtum na kasar Sudan a ranar 4 ga wata, inda ministocin suka yi kira ga bangarori daban daban na kasar Libya da su dakatar da yake-yake cikin hanzari da komawa teburin shawarwari domin maido da zaman lafiya da sulhuntawa a tsakaninsu.

A cikin sanarwar karshe, mahalarta taron, sun bayyana damuwarsu kan wahalar da jama'ar kasar Libya ke fuskanta sakamakon tsanantawar rikice-rikicen dake a kasar, kana sun bukaci bangarori daban daban na kasar da su yi watsi da tada zaune tsaye da gudanar da shawarwari domin sassantawa tsakanin dukkan al'ummar kasar nan da nan. Sanarwar ta jaddada girmama kowane zaben jama'ar kasar Libya, da nuna goyon baya ga halaltacciyar gwamnatin kasar, da sake kafa da kyautata rundunar sojojin kasar da 'yan sanda, ta yadda za a samu zaman lafiya da na karko da bunkasuwa a kasar.

Ban da wannan kuma, sanarwar ta jaddada cewa, tilas ne a girmama ikon mallaka da cikakken yankin kasar Libya, da tabbatar da zaman lafiya a fannin siyasa, da kin amincewa da tsoma bakin kasashen waje kan harkokin cikin gida na kasar Libya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China