Ya ce a ranar 10 ga watan Oktoba, dakarun Zintan dake goyon bayan kungiyar 'yan ba ruwan mu sun kai hari ga garin Kikla, mai nisan kilomita kimanin 150 da birnin Tripoli, wanda kuma ke karkashin ikon dakarun Fajr Libya dake goyon bayan kungiyar masu kishin addini.
Wani mutum dake aiki a wani asibitin dake garin Kikla ya ce rikicin na ranar 3 ga wata, ya haddasa mutuwar mutane a kalla 142, baya ga wasu kimanin 518 da suka jikkata. (Zainab)