in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 36 suka mutu sakamakon rikicin da aka yi a Benghazi
2014-11-02 15:25:54 cri
A ranar Asabar, hukumomin soja da na kiwon lafiya na kasar Libya sun ce, an yi arangano tsakanin dakarun kungiyoyi biyu na kasar a kokarin da suke na neman kwace birnin Benghazi dake gabashin kasar, lamarin da ya yi sanaddiyar mutuwar mutane a kalla 36.

Kakakin sojan kasar Libya Ahmad Al-Mismari ya gayawa kamfanin dillancin labaru na Xinhua a wannan rana cewa, kungiyoyi masu ra'ayin sakulanci, ciki har da sojojin musamman na kasar, da kungiyar dake goyon bayan janar Haftar suke rike da yawancin yankunan dake Benghazi, amma wasu yankunan dake yammaci da kudancin birnin a yanzu haka suna hannun dakarun fararen hula masu kishin addini.

Majiyar bangaren asibitoci na birnin Benghazi ta tabbatar da cewa, mutane 36 ne suka mutu a sakamakon rikicin da aka yi a wannan rana.

Tun daga ranar 15 ga watan Oktoba zuwa yanzu, mutanen da suka rasu sakamakon rikicin a tsakanin dakaru na kungiyoyin biyu a Benghazi ya wuce 250. (Bilkisu)
 
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China