in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira ga shugabannin Libiya da su karfafa shawarwarin maido da zaman lafiya
2014-10-12 16:39:00 cri
Babban sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon, ya yi kira ga bangarori daban daban masu ruwa da tsaki a kasar Libiya da su fara yin shawarwarin zaman lafiya domin warware rikici da maido da zaman karko a cikin kasar. Mista Ban ya yi wannan kalami, a yayin wata ziyarar a Tripoli, babban birnin Libiya a ranar Asabar, inda ya samu rakiyar wakilinsa na musammun dake Libiya, mista Bernardino Leon.

A cewar wata sanarwa da kakakinsa ya gabatarwa 'yan jarida, sakatare janar zai gana a cikin wannan rana da mataimakin shugaban majalisar dokokin Libiya da kuma mambobin zauran wakilai da suka janye daga zaman tarurukan majalisar dokoki.

Ministan harkokin wajen kasar Italiya, har ma da wakilan musammun na sauran kasashe za su halartar wannan taro.

Ziyarar shuagaban MDD, ta zo daidai bayan nasarar kokarin wakilinsa na musammun, da kuma tawagar MDD dake kasar Libiya (MANUL) domin sake maido da tattaunawa tsakanin 'yan majalisun kasar. Wannan tattaunawa da aka fara a ranar 29 ga watan Satumba, an kafa ta bisa tushen ka'idojin gaskiya, kaucewa nuna bambanci da watsi da ta'addanci, kuma ta kasance shirin farko wajen warware rikicin kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China