Mutane wadanda suka fito daga wurare daban daban na kasar Amurka sun dauki manyan ababen hawa domin isa Washington DC, inda suka yi zanga-zanga cikin ruwan sanyi. Shugabannin masu wannan zanga-zanga sun nemi a daidaita wannan matsalar ta nuna bambancin launin fata da ta dade tana kasancewa a lokacin da 'yan sanda suke gudanar da aikinsu bisa doka ta hanyar gyara dokokin kasa kan wannan matsala.
A kwanan baya, ma'aikatar shari'a ta kasar Amurka ta fitar da wata sabuwar manufa bisa kokarin hana sake abkuwar irin wannan matsalar.
A waje daya, gwamnatin Obama ta yi kira ga majalisun dokokin kasar da su kebe karin kudi ga aikin horas da 'yan sanda, da kuma samar wa 'yan sanda na'urorin daukar bidiyo da za su iya bayyana yadda suke gudanar da aikinsu bisa doka.
Bugu da kari, an kuma yi irin wannan zanga-zanga a birnin New York da sauran biranen kasar . (Sanusi Chen)