in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zanga-zanga ta sake barkewa a Ferguson dake birnin St. Louis na Amurka
2014-08-31 16:45:06 cri

Rahotanni daga jihar Missourin kasar Amurka, na cewa masu zanga-zanga sun sake kwarara kan tituna a unguwar Ferguson dake birnin St. Louis, domin nuna fushin su game da kisan Michael Brown, matashin nan bakar fata da wani dan sanda farar fata ya harbe makwanni uku da suka gabata.

Zanga-zangar ta ranar Asabar dai ta samu halartar daruruwan mutane, wadanda suka rika bayyana rashin gamsuwa da kisan matashin da ma wasu batutuwa da suka shafi ayyukan 'yan sanda.

Iyalan Michael Brown sun wuce gaba ya yin da ayarin masu zanga-zangar ke isa wurin da aka harbe matashin. Kafin daga bisani su yi jerin gwano zuwa kofar ofishin 'yan sandan yankin na Ferguson, inda suka yi gangamin nuna fushin su.

Tuni dai wasu mutane shida daga jihar ta Missouri suka gabatar da kara gaban kuli kan yadda 'yan sanda suka yi amfani da karfi da makamai fiye da kima, suna masu zargin 'yan sanda da kitsa wasu al'amura tsakanin ranekun 11 zuwa 13 ga wata, tare da amfani da karfin tuwo, da tsare mutane ba bisa ka'ida ba.

A cewarsu, wadannan 'yan sanda sun keta hurumin jama'a, don haka suka bukaci da a biya diyya, da yawan ta ya kai dalar Amurka miliyan 40.

A wani ci gaban kuma, jaridar Los Angeles Times ta ce mai gabatar da kara, ya zargi 'yan sanda da harbin sa da harsasan roba, suka kuma rika dukan sa, tare da fesa masa hayaki mai sa hawaye, duk kuwa da cewa bai nuna wata alama ta bijirewa kame ba.

Dadin dadawa, sauran masu karar sun ce, 'yan sanda sun harbe su da harsasan roba, ba tare da la'akari da mika wuya da suka yi ba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China