Ranar Jumma'a 5 ga wata, ofishin babban manzon musamman na MDD mai kula da harkokin hakkin dan Adam ya nuna kulawa kan hukuncin da wata kotun wurin ta yanke wa wani dan sandan birnin New York na kasar Amurka farar fata, inda kotun ta wanke sa, dan sandar dai ina zarginsa da shake wani ba'amurke dan asalin nahiyar Afirka.
Madam Ravina Shamdasani, kakakin ofishin ta bayyana a wannan rana cewa, ofishin babban manzon musamman na MDD mai kula da harkokin hakkin dan Adam na sa kulawa sosai kan sakamakon da ya biyo bayan wannan hukuncin da aka yanke a birnin New York.
Madam Shamdasani ta kuma kalubalanci mahukuntan kasar Amurka da su yi kokarin kawar da rashin jin dadi da al'ummar kasar suka dade suna nunawa dangane da illolin da bambancin launin fata suke haddasawa a wajen aiwatar da dokoki, kuma ya kamata mahukuntan Amurka su yi nazarin ainihin dalilin da ya sa hakan. (Tasallah)