Firaministan kasar Britaniya David Cameron ya bayyana cewa, yaki da ta'addanci ta hanyar cin zarafin mutane da amfani da wasu hanyoyin keta hakkin dan Adam ba zai yi wani tasiri ba tare da mai da hannu agogo baya. Ya ce, keta hakkin dan Adam, ba zai taimaka ga yakin da ake da ta'addanci ba.
Shi ma ministan harkokin wajen kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana cewa, yadda hukumar CIA ke gallazawa fursunoni ya sabawa dokokin 'yancin bil-adama da kuma tsarin demokuradiyya, tilas ne a yi watsi da irin wannan mataki. Ya ce, ba a amince da wannan mataki ba duk da cewa, ana aikata shi yayin da ake yin yaki da ta'addanci, wannan kuskure ne.
Manazarci a cibiyar nazarin tsare-tsare ta kasar Masar ya bayyana cewa, yadda hukumar CIA ke cin zarafin fursunoni ya bayyana cewa, kasar Amurka tana aiwatar da ma'auni biyu kan hakkin dan Adam. A hakika dai, batun hakkin dan Adam ita ce muhimmiyar hanyar da kasar Amurka ta ke amfani da ita don cimma muradunta. (Zainab)