in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a mai da hankali kan farfado da kasashen da suke fama da cutar Ebola
2014-12-06 16:44:51 cri

Ranar 5 ga wata, Ban Ki-moon, babban magatakardan MDD da Sam Kahamba Kutesa, shugaban babban taron MDD karo na 69 sun yi kira ga kasashen duniya da su mai da hankali da kuma ba da taimako wajen farfado da tattalin arziki da zaman al'ummar kasa a kasashen yammacin Afirka, bayan taimaka musu wajen yaki da cutar.

A cewar Ban Ki-moon, bayan barkewar cutar Ebola, kasashen Guinea, Liberiya da Saliyo sun dakatar da bunkasar tattalin arzikin kasashen nasu uku. Don haka ya yi kira ga kasashen duniya da su mara musu baya wajen samun saurin farfadowa, kamar yadda kasashen duniya suke namijin kokarin taimaka musu wajen samun nasarar yaki da cutar Ebola.

Har wa yau kuma, mista Kutesa ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, matsalar yaduwar cutar nan ta Ebola ta jaddada muhimmanci da wajibcin raya muhimman ababen more zaman rayuwar jama'a masu inganci, wadanda za su mayar da martani yadda ya kamata cikin hanzari. Baya ga yaki da cutar Ebola, ya zama tilas a kara mai da hanklai kan sake gina kasashen da cutar ta shafa ta fuskar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa.

Haka zalika kuma, mista David Nabarro, manzon musamman na MDD mai kula da batun kwayar cutar Ebola ya yi bayanin cewa, yaduwar cutar Ebola ta raunana karfin gwamnatocin kasashen Guinea, Liberiya da Saliyo na samun kudaden haraji. A sa'i daya kuma, yawan kudaden da gwamnatocin kasashen 3 suka kashe wajen yaki da cutar ya karu da misalin kashi 30 cikin dari. Don haka wajibi ne kasashen duniya su kara hada kansu wajen fara mara wa wadannan kasashe baya nan take ba tare da bata lokaci ba da su daidaita matsalolin rashin guraben aikin yi, raguwar kudaden haraji, rashin isassun 'yan kwadago da bunkasa tattalin arziki maras karfi da dai sauransu. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China