Shugaban bankin duniya, Jim Yong Kim ya isa kasar Ghana a ranar Talata a wani rangadin da ya shafi kasashen yammacin Afrika hudu. Bayan Ghana, zai isa kasashen nan uku da cutar Ebola ta fi muni, wato Saliyo, Liberiya da Guinee, in ji sanarwar cibiyar bankin duniya dake Ghana.
A cewar sanarwar, dokta Kim zai tattauna tare da shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama da sauran manyan jami'an kasar, kana zai gabatar da gamsuwar cibiyar bankin duniya dake Ghana kan matsayinta na mai ba da jagora kan martanin shiyyar wajen yaki da cutar Ebola. Tattaunawa tare da shugaba Mahama za ta mai da hankali kan kalubalolin tattalin arzikin Ghana da kuma muhimman matsayin da masu ruwa da tsaki suke dauka, har ma da gwamnati, abokan huldar ba da tallafi, bangaren masu zaman kansu da fararen hula domin murkushe Ebola.
Haka kuma, dokta Kim zai gana da wani gungun shugabannin kamfanoni masu zaman kansu dake gudanar da harkokinsu a shiyyar yammacin Afrika domin tattaunawa kan illar da cutar Ebola ta janyo wa masana'antu, musammun ma kananan kamfanoni.
Ana hasashen cewa, asarar da annobar cutar Ebola ta janyo wa tattalin arzikin kasashen dake kudu da hamadar Sahara ta kai dalar Amurka biliyan uku zuwa biliyan hudu.
A yayin ziyarar baya bayan nan a kasar Ghana a karshen watan Oktoba, mista Kim ya kara samar da karin tallafin kudi na dalar Amurka miliyan 100 domin yaki da cutar Ebola a shiyyar yammacin Afrika, kudin da suka kai a halin yanzu zuwa dalar Amurka miliyan 500, jimillar kudin da bankin duniya ya ware domin yaki da cutar Ebola. (Maman Ada)